Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 390 Can Cikin Baitalahmi, Yesu Ya Zo Lyrics
1
Can cikin Baitalahmi, Yesu ya zo
Kamar ɗan jariri Allah ya iso.
Darajar ta sama ya bar domin mu
Ya yarda shi zama mutum talaka.
2
Ba gidan mai arziki ko sarauta
Ba darajar duniya Yesu ya zaɓa
Ba wurin mafaka domin Ɗan Allah
Wanda ya yi sama da duk duniya.
3
Ya Yesu Mai Ceto, gareka mun zo,
Mun kawo yabonmu, Kai ne mu ke so
Ƙamnar muke ba ka, da godiyarmu,
Karɓi zukatanmu, ka yi mulkinmu.
