Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 39 Duk Nufina da Zuciyata, Ya Allah, Tone Su Lyrics
1
Duk nufina da zuciyata, ya Allah, tone su.
Asiran rai da tunani, ka auna su yanzu.
2
Mugun abu da tayarwa, ka taka, kashe su.
Kada ka rage abu ɗaya mai musun ƙaunarka.
3
Inda na ƙi sarautarka a cikin raina dai,
Amshi mabuɗi, shigo nan, ka share lolokai.
4
Kowane hali riƙaƙƙe da mugun tunani,
Sarƙoƙin bautar Iblis ne, yau sai ka kwance su.
5
Maƃoya duk na tussan rai inda na ƙi ka da,
Karƃi sarautarsu yanzu, Yesu Mai Mulkina.