Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 386 Ban Gane Yadda Zunubai na Adam Sun Rayu Lyrics
1
Ban gane yadda zunubai na Adam sun rayu
A cikin dukan mutane babba ko ƙarami.
KORUS
Amma ga shi, nan, Magana ce ta Allah
Ta Ubangiji, na gaskanta shi.
Na karanta shi nan, na gaskanta shi
Ya ishe ni, ya isa.
2
Ban gane yadda Allahmu ya sabko duniya nan
Ya ɗauki jikin ƴan Adam ya bar sama a can.
Korus
3
Ban gane yadda Allah fa ya aza nawa laifi
A bisa Ɗansa a giciye, nasarata ya ci.
Korus
4
Ban gane yadda Allah fa ya buɗe kabari
Yesu ya biya pansata, rai na har abada.
Korus
5
Ban gane yadda jininsa ya wanke zunubi
Ya ba ni tashi daraja, yanzu ɗansa ni ke.
Korus.
6
Ban gane yadda wata rana Yesu zai fyauce ni
Shi kai ni can wurin Uban da sauran masu bi.
Korus