Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 383 Ba Wuri Domin Yesu Can Baitalhami Lyrics
1
Ba wuri domin Yesu can Baitalhami
Sai wurin dabobbi
Ba wuri a duniya domin Ɗan Allah
Ba wurin kwantawa.
KORUS
Sai giciye an ba Maɗaukaki
Sai kumya, kabari
Yau yana ƙwanƙwasa a zuciyarka.
Bari ka ce masa, “Shigo”
2
Ya jira, ya kira ƙofar zuciyata
Na kyale ƙamnarsa,
Amma Mai Cetona ya ji tausayina
Ya jawo ni wurinsa.
Korus
3
Ya Almasihu, ina yarda da kai
Na faɗi aibina
Ka wanke ni, gafarta duk laifina
Ka zama Mai mulkina.
Korus
