Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 38 Mun Gode Wa Allah da Dukan Zuciyarmu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 38 Mun Gode Wa Allah da Dukan Zuciyarmu Lyrics

 

1
Mun gode wa Allah da dukan zuciyarmu,
Da waƙa mai daɗi domin duk ayyukansa.
Tun muna jarirai, albarkarsa ‘na nan.
Da duk alheransa, yanzu ya dube mu.

2
Rayayyen Allahnmu tare da mu zai zauna.
Muddar rayukanmu, shi zai albarkace mu.
Kullum da alherai zai kiyaye mu duk.
Zai tsare ƴaƴansa daga hatsari duk.

3
Yabo da hamdala ga Allahnmu na Sama,
Da Ɗa Mai Cetonmu, Ruhunsa mai bishe mu. Duniya da Sama duk suna ta yabonsa
A da, da yanzu kuwa, nan gaba abada.

Exit mobile version