Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 378 Aure Na Masu Bi, Aure Ne Mai Tsarki Lyrics
1
Aure na masu bi aure ne mai tsarki, ku ƙaunace juna har abada
Ubangiji Allah shi ne ya kafa aure ya ce mu yi aure a duniya
KORUS
Ku zama ɗaya cikin zamanku, Amarya yi bayayya
Ango ka ƙaunaceta gidan ku zai zama da Albarka
2
Ango na murmurshi, Amarya na murmurshi, dono yau suna cikin alkawali
Mu masubi duka muna tayaku murna mune shaidun wannan aure a yau.
Korus
3
Ku ba juna shawara juna yin addu’a, ku zuba ido ga Yesu Kristi,
Ko cikin wahala ko cikin jin daɗi ku kasance da ƙaunan junan ku.
Korus
4
Macen kirki takan faranta ran mijinta mara kirki takan zama ciwo
Amarya ki zama mai faranta ran mijinki, mijinki zai kasance da murna.
Korus
5
Samari da ƴan mata sai ku yi addu’a don ku yi nasara da magabci.
Mu masu bi duka muna yin addu’a Ubangiji y baku nasara.
Korus