Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 37 Yabo Ga Allahnmu, Shi Ne Mahaliccin Kome Lyrics
1
Yabo ga Allahnmu, shi ne mahaliccin kome !
Ya raina, yabe shi, shi ne Mai Ceto, mai kiwo.
Zo, masu ji,
Maza da mata ku zo,
Ku guso nan, ku yabe shi.
2
Yabo ga Allahnmu, mai mulkin Sama da duniya!
Ya kiyaye mu ƙarƙashin fukafukan kansa.
Ba ka ji ba?
Bukatar kowa ya biya
Ta wurin ikon ƙaunarsa.
3
Yabo ga Allahnmu, wanda ya tsare mu duka !
Kullum jinƙai da alheri su kan kiyaye mu.
Lura da kyau.
Kome Mai Iko ya iya,
Don ƙaunarsa a gare mu.
4
Ya raina duka, ka yabi Ubangiji Allah.
Yara da manya ku zo a gabansa da waƙa.
Bari “Amin”
Shi fito bakinmu duk.
Har abada mu yabe shi.
