Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 369 Allah Ya Yi Ҡamnar Mu Lyrics
1
Allah ya yi ƙamnar mu, har ya aiko tilonsa
Don ya shirya hanya zuwa gun Uba,
Sai ku bad gaskiya, sai ku juyo wurinsa
Shi zai ba mu sabon Rai, sai ku ji.
KORUS
Yesunmu yana da rai,
Halleluya Mai Cetonmu na da Rai,
Shi zai sake dawowa
Don Shi kai mu sama can
Pansassu da Cetattu nasa ne.
2
Ku iyayen mu, kun ji, sai ku koya mana yau.
Labarin Mai Ceton koyaushe
Kada mu bar tafarkinsa har mu zama batattu,
Za mu shaida sunanka, sarkinmu.
Korus
3
Sai in ji, in dinga ji labarin Mai Ceton nan
Wanda Allah ya aiko domina.
Shi ya sha wahalata, don ya ba ni wannan rai
Yesu ni ke bi yanzu, shi kaɗai.
Korus
4
Masu rai da mattatu, za su ganka Sarkinmu,
Farin ciki za mu yi dominka.
Kai ne Ɗan Maɗaukaki, begenmu ne zuwanka.
Za mu raira waƙarmu. Zo yanzu.
Korus
5
Duk annabcin da an yi,
Yanzu suna cikawa.
Muna jiran zuwanka, Sarkinmu.
Aikinmu da dukiyarmu, dukan wannan banza ne.
Zo, ka ba shi zuciyarka tun yanzu.
Korus
