Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 367 Allah Ya Kira Shugaba Lyrics
1
Allah ya kira shugaba
Na duk mala’ikun sama
Ya ce “Zan aike ka a duniya”
Ya ce “Na yarda Ubangiji”
“Ga ni, ka aike ni ko yanzu.”
2
“Ka sabka, ka je duniya”
Za ka iske budurwa,
Sunnanta Maryamu ne.”
Mala’ika ya bar gaban Allah,
Mala’ika ya bar gaban Allah,
Ya zo, ya iske Maryamu.
3
Ya ce, “Allah ya aiko ni
Da saƙonsa mafi tsarki
Shi ne Yesu Ruhunlahi,
Shi za ya shiga mahaifarki,
Shi za ya shiga mahaifarki
Shi ne ‘Allah tare da mu”.
4
Buduruwa ta razana
Ta ce, “Ni buduruwa ce
Ban taɓa shafe namiji ba”.
Mala’ika ya ce, “Gaskiyarki,”
Mala’ika ya ce, “Gaskiyarki,”
“Ba ki taɓa shafi miji ba”.
5
“Ai, wannan ikon Allah ne,
Ni ma, na ji tsoro ƙwarai.
Da ni da ke, duka ɗaya ne.
Mu bar wannan ga Ubangiji,
Mu bar wannan ga Ubangiji,”
In ji Mal’ika Jibra’ilu.
6
Buduruwa ta ɗauki ciki
Ta wurin Ruhun Mai Tsarki
Ta haifi Macecin ƴan Adam,
Shi ne Yesu Almasihu,
Shi ne Yesu Almasihu,
Shi za ya shirya duniyan nan.