Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 364 Alhajai na Almasihu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 364 Alhajai na Almasihu Lyrics

 

1
Alhajai na Almasihu
Hanyar ɗaya mu ke bi
Kome wuya, kome ƙunci
Za mu ƙasar alkawali.

2
Hasken Yesu Ubangiji
Yesu walƙiya wajenmu
Yana koran duhun hanya
Yana cika zuciyarmu.

3
Ɗaya ne Ubangijinmu
Ɗaya ce bangaskiyarmu
Ɗaya ne kuwa begenmu duka
Ɗaya kuma yancinmu.

4
Waƙar masu bi ce ɗaya
Kome dubban bakinmu
Ɗaya ce zumuntar hanya
Ɗaya ce jawabinmu.

5
Ɗaya ce sujadar taron
Cikin ƙasar sama can
Inda Alahnmu Mai Ҡamna
Yana mulki abadan.

Exit mobile version