Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 363 Albishirin Ku Mutane Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 363 Albishirin Ku Mutane Lyrics

 

KORUS
Albishirin ku mutane
Salama yau ga duniya
Gama an haifa mana Mai Ceto
Emmanuel Allah, tare da mu.

1
Malaiku da suka gani
Suka rera halleluya
Sai suka shaida ma makiyaya
Haifuwar Yesu Ubangiji.
Korus

2
Makiyaya da suka ji labari
Suka bar dabbobinsu
Suka je domin su ga mai ceto
Yesu makiyayi mai kyau.
Korus

3
Shehuna da gabas sun gani
Tauraro Ubangiji
Suka tafo bisa rakumansu
Don su gaida sarkin sarauta.
Korus

4
Tun da kun ji labari
Na haifuwar Ubangiji
To sai ku shaida ma mutane
Haifuwar mai ceton duniya.
Korus

Exit mobile version