Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 36 Mu Zo da Murna Dayawa Lyrics
1
Mu zo da murna dayawa,
mu ta da muryarmu,
Mu rera waƙa sabuwa,
waƙar mala’iku.
2
Ubangiji ya cancanci
ya karƃi yabonmu.
Gama lalle ya rinjayi
Shaiɗan makiyinmu.
3
Ya cancanta, Mai Cetonmu,
ya karƃi albarka.
Shi ne ya mutu dominmu,
ya ka da mutuwa.
4
Albarkaci Ubangiji,
ku talikansa duka.
Mai iko ne, mai girma shi,
yanzu, har abada.