Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 357 Akwai Littafi A Sama Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 357 Akwai Littafi A Sama Lyrics

 

1
Akwai littafi a sama
Wanda Allah ya yi
Inda an sa sunayen duk masu bi.
In babu sunanka
A littafin nan
Ba za a karɓe ka wurin Mai Tsarki can.

KORUS
An sa sunana can
Cikin Littafin Rai
Tun da na karɓi Yesu
An sa sunana can.

2
Da na zamna a duhu
Ban san haryarsa ba
Sai an ba ni labarin Yesu Mai Cetona
Sai na tuba, na bi shi
Na bar duk laifina
Shi kuwa ya sa sunana a Littafinsa can.

Exit mobile version