Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 355 Akwai Aiki Domin Mataye Lyrics
1
Akwai aiki domin mataye,
Wurin mutane kusa da mu
Sai mu yi da aminci sosai
Kada dowa ya rasa ceto.
KORUS
Aminci…..aminci,
Cikin aikinmu domin Uba,
Aminci…..aminci,
Har mu kai gidan Allah a can.
2
Akwai kira domin mataye
Daga ƴanuwarnmu da nisa,
Sai mu aiki da taimakonmu
Da aminci da addu’a kuwa.
Korus
3
Akwai iko domin mataye,
Cikin Yesu Ubangijinmu
In mu kawasda zunubi duk
Za ya kira mu amintattu !
Korus