Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 353 Aike da Abincinka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 353 Aike da Abincinka Lyrics

 

KORUS
Aike da abincinka, a bisa ruwaye,
Gama za ka same shi, bayan ƴan kwanaki.
(2x

1
Ga wasu bayi uku, aka yi kiransu,
Ubangijinsu ya damƙa, masu dukiyarsa.
Ga wani talent biyar, ga wani talent biyu,
Ga wani talent ɗaya, gwalgwadon kowa.
(Solo: “Ɗan’uwa.”

Korus

2
Bawa mai talent biyar, da mai talent biyu,
Suka fidda tsoro, suka yi bangaskiya.
Suka jujjuya kuɗin, suka sami riɓa,
Ubangijinsu ya sa, masu albarka.
(Solo: “Ƴar’uwa”

Korus

3
Bawa mai talent ɗaya, shi kuwa ya ji tsoro,
Ya yi haƙi a ƙasa, ya ɓoye talent nan.
Ubangijinsa ya ce, kai mugun bawa,
Ku jefa cikin, baƙin duhu.
(Solo: “Duka”

Korus
4
Ƴan’uwa mu yi koyi, da mai talent biyar,
Mu fidda tsoro, mu yi bangaskiya.
Mu aike da abincinmu, a bisa ruwaye,
Gama za mu same shi, bayan kwanaki.
Korus

Exit mobile version