Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 35 Ya Almasihu, Mulkinka Zai Fi Duka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 35 Ya Almasihu, Mulkinka Zai Fi Duka Lyrics

 

1
Ya Almasihu, mulkinka
Zai fi duk sauran mulkoki,
Zai tabbata har abada,
Madauwami ne mulkinka.

2
Ga ƙoshin rai a mulkinka,
Albarka kuwa a yalwace,
Ga ƙauna, murna, lafiya,
Ga ƴanci kuma cikakke.

3
Yi yabonsa babu fasawa,
Samari, yara, tsofaffi.
Mulkinsa yana da girma fa,
Sunansa kuwa mai tsarki ne.

4
Albarka ga Ubangiji,
Mai mulkin dukan duniya.
Ƴan Adam duk, ku neme shi
Mai jinƙai ne har abada.

Exit mobile version