Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 344 Sai Ku Tashi, Duk Ƴan’uwa Lyrics
1
Sai ku tashi, duk ƴan’uwa, ji kiran Nijeriya!
Da aminci, ƙwazo, ƙauna, yi wa tasar hidima,
Ƙoƙarin jarumai na dā ba banza ya ke ba!
Da dukan ƙarfinku,
Tsare salama da ƴanci, da ɗayantuwarku !
2
Ya Mahaliccin duniya, ka bi da manyanmu
Har su ciccika nufinka. Taimaki duk ƴaƴanmu
Su girma cikin gaskiya, ƙauna, da adalci.
Ka mai da Nijeriya
Wurin da kowa zai zauna da kwanciyar hankali!
