Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 342 Muna Roƙon Ubangiji Allah Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 342 Muna Roƙon Ubangiji Allah Lyrics

 

1
Muna roƙon Ubangiji Allah
Domin salamar Yahudawa yau.

2
Al’umma ce wadda ka zaƃa fa
Domin su zama mutanenka dai.

3
Amma sun ƙi su karƃe ka a dā.
Sun juya maka baya, sun ƙi ka.

4
Ka hore su, ka warwatsad da su
A fuskar duniya duka ko’ina.

5
Yanzu kuma ga lokaci ya yi
Da za su koma Urushalima.

6
Yanzu ga su a cikin zafin rai
Har lalle ba su san abin yi ba.

7
Mun sani fa kai kana ƙaunarsu,
Ka taimake su, mutanenka yau.

Exit mobile version