Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 341 Ya Ubangijinmu, Dube Mu Duk Yanzu Lyrics
1
Ya Ubangijinmu, dube mu duk yanzu
A gabanka.
Sarkin sarakuna, mai iko duka kuwa,
Karƃi sujadarmu, Ubangiji.
2
Roƙonka mu ke yi don masu mulkinmu,
Ka cece su.
Tsawanta ransu kuwa, su ma a zuciyarsu
Su nemi fuskarka, Ubangiji.
3
Daidaita hanyarsu cikin sarauta fa,
Ka riƙe su.
Ba su albarkarka, girma da lafiya,
Iko da nasara, Ubangiji.
4
Tuna da ƙasarmu, ka san bukatarmu
A duniyan nan.
Kai ne Mai Cetonmu, kai ne shugabanmu,
Bishe mu duk yanzu, Ubangiji.