Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 340 Ya Ubangiji, Allahnmu, Ka Sa Albarkarka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 340 Ya Ubangiji, Allahnmu, Ka Sa Albarkarka Lyrics

 

1
Ya Ubangiji, Allahnmu, ka sa albarkarka
Yanzu a bisa shugabanni da dukan iyalansu.

2
Ka ƙara musu aminci, alheri da soyayya.
Salama duk da lafiya su daɗu a mulkinsu.

3
Ka ba su ruhun hikima da ruhun ganewa.
Ka kafa dukan maganarsu bisa ga shari’arka.

4
Domin a cikin mulkinsu, kome da za su yi
Shi daidaita da nufinka, nufi mai tsarki.

5
Hakanan mu jama’arsu, mu riƙa yin godiya
Gare ka kullum, har da su, a cikin duniya duk.

6
Ya Allah Uba, Allah Ɗa, Allah Ruhu kuma,
Mu ba ka dukan daraja, ya Allah Triniti.

Exit mobile version