Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 34 Ya Maɗaukaki na Allah Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 34 Ya Maɗaukaki na Allah Lyrics

 

1
Ya Maɗaukaki na Allah,
Zan yi yabonka ƙwarai.
Kai, ka shafe zunubaina,
Kai, ka ba ni sabon rai,
Halleluya, Halleluya,
Girma duka naka ne.

2
Mun yabe ka don alheri
Zuwa kakaninmu da.
Yau da gobe ka ke nan fa,
Ƙaunarka ta tabbata.
Halleluya, Halleluya,
Ɗaukaka amincinka,

3
Makiyayi mai tausayi,
Wanda ya san halinmu,
Daga dukan jarabobi
Ya fisshe mu lafiya.
Halleluya, Halleluya,
Wa ke jinƙai kamarka?

4
Ɗaukaka ga Ubangiji,
Kai kaɗai mai adalci,
Kai ne farko, kai ne ƙarshe,
Ƙauna, Iko, Gaskiya.
Halleluya, Halleluya,
Mun yi maka sujada.

Exit mobile version