Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 338 Mu Bubbuɗe Zukatanmu Lyrics
1
Mu bubbuɗe zukatanmu
Ga Ubangiji Allah,
Mu miƙa mar hadayarmu,
Mu yi masa sujada
Domin yalwar wadatarsa
Da duk amfanin gona.
Mun gode wa Ubangiji
Domin kyautansa duka.
2
Mun girbe dukan gonaki,
Ga dawa cikin rumbu.
Mun tara dukan amfani
Na aikin hannuwanmu.
Wannan ne fa abincinmu
Na rai a wannan duniya.
Kullum fa ka ciyad da mu
Da abinci na ruhu.
3
Mun yi wahalar damuna,
Mun sha gajiya ainun,
Amma a ƙarshen yini fa
Ka ba mu damar hutu.
Ka sa mu zama zaƃaƃƃu
Na ƴaƴan fari naka,
Mu cika aikinka a nan,
Mu shiga hutu naka.
4
Ƙasar can mai albarka ce,
Ƙasa ta mulkin Allah.
Can dai akwai itacen rai,
Da kuma kogin Allah.
Duk tsarkaka sun taru can,
Mu kuma za mu bi su,
Mu yi ta yabon Allah can,
Don ya albarkace mu.
