Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 335 Damuna Ta Faɗi, Ana Ta Yin Ruwa Lyrics
1
Damuna ta faɗi, ana ta yin ruwa
Daidai shukar iri, ƙasa ta yi kyau.
Sai mu yi wa Yesu shukarsa a gona,
Kada shi ya ga mai fasa aiki yau.
KORUS
Farar zuciya, farar zuciya,
Lalle za mu samu in kaka ta yi,
Manyan dammuna, manyan dammuna,
Lalle za mu samu in kaka ta yi.
2
Ko da rashin ruwa, ko da wani abu
Wanda ya yiwu ya ƃata mana rai,
Sai mu dinga noma, muna roƙon Allah,
Kwana tashi, sai hatsi ya fid da kai
Korus
3
“Sai ku yi addu’a,” in ji Almasihu,
“Sai ku roƙi wanda girbi nasa ne,
Masu iya aikin girbi dai ya aiko
Zuwa gonar hatsi, domin ya nuna!”
Korus