Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 334 Ya Allah, Muka Shuka Iri A Gonarmu Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 334 Ya Allah, Muka Shuka Iri A Gonarmu Lyrics

Hymn 334 Ya Allah, Muka Shuka Iri A Gonarmu Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 334 Ya Allah, Muka Shuka Iri A Gonarmu Lyrics

 

1
Ya Allah, muka shuka iri a gonarmu,
Amma, ya Ubangiji, ka ba da amfani.
Ga hatsi, ga dankali, wake da shinkafa.
Su muka yi ta noma, sun kuma nuna yau.
Kai Mahaliccinmu, ka ba mu kyautarsu,
Mu yi godiya, mu yi godiya, domin amfaninsu.

2
A gona mu ke aiki, amma, ya Allahnmu,
In ba ka sa albarka ba, ina amfaninsu?
Ka ba da hasken rana, da ruwa mai yawa,
Kai ne ka shirya ƙasa da daɗin iska kuwa.
Kai Mahaliccinmu, ka ba mu kyautarsu,
Mu yi godiya, mu yi godiya domin amfaninsu.

3
Amma, ya Ubangiji, dubi zukatanmu,
Yanzu ta wurin Ruhunka, maishe su gonarmu.
Maganarka ce iri, ka ba mu ikonka
Domin ta daɗa girma, ta shaida zamanka.
Ya Mahaliccinmu, ka sa albarkarka,
Har raina duk ya lura da irin Maganarka.

4
Ni, zan tafi wurinka sa’ad da na rasu,
Zan kai amfanin gona, gona ta zuciyata.
Ga ƴaƴan raina kuma, ƴaƴan Maganarka,
Gare ka duk zan kawo do min albarkarka.
Ya Mahaliccinmu, ka sa albarkarka,
Har raina duk ya lura da irin Maganarka.

Post navigation

Previous: Hymn 547 Ya Allahna Lyrics
Next: Hymn 148 Wanda Ya Ke Neman Ceto Daga Zunubi Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version