Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 333 Ubangijinmu Ya Raka Ka Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 333 Ubangijinmu Ya Raka Ka Lyrics

 

1
Ubangijinmu ya raka ka,
Ikon Allah ya ƃoye ka,
Hannunsa ya taimake ka,
Har ya sake tara mu da kai.

KORUS
Har ya tara mu, ko a duniyan nan,
Ko a cikin Sama ne,
Har ya tara mu, har ya tara mu,
Ubangijinmu ya raka ka.

2
Ubangijinmu ya raka ka.
Ko jaraba ta dame ka,
Ubangiji ya cece ka,
Har ya sake tara mu da kai.
Korus

3
Ubangijinmu ya raka ka.
Ko wahala ta same ka,
Ubangiji ya fisshe ka,
Har ya sake tara mu da kai.
Korus

4
Ubangijinmu ya raka ka.
Ikonsa ya agaje ka,
Ƙaunarsa ta kewaye ka,
Har ya sake tara mu da kai.
Korus

Exit mobile version