Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 332 Akwai Gidan Zamana Cikin Birnin Allah Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 332 Akwai Gidan Zamana Cikin Birnin Allah Lyrics

 

1
Akwai gidan zamana cikin birnin Allah.
Ba zai rushe ba daɗai, babu dare ma can.

KORUS
Za ya shafe hawaye, babu sauran mutuwa,
Ba lissafin shekaru, babu dare ma can.

2
Ƙofofi Iu’u-Iu’ai ne a birnin Allah
Hanya duk zinariya, babu dare ma can.
Korus

3
Itace mai ƴa ƴa kuwa yana birnin Allah.
Za mu duba kogin rai, babu dare ma can.
Korus

4
Ba bukatar rana can cikin birnin Allah.
Yesu shi ne Haskenmu, babu dare ma can.
Korus

Exit mobile version