Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 331 Ka Haƙura, Ya Raina, Haƙura Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 331 Ka Haƙura, Ya Raina, Haƙura Lyrics

 

1
Ka haƙura, ya raina, haƙura.
Ubangiji kuwa yana wajenka,
Ka haƙura, kome dai ya same ka,
Azaba, sakewa, ko damuwa.
Ga Allahnka zai shirya mafakatka,
A ƙarƙashin fukafukansa kuwa.

2
Ka haƙura, ya rai na, haƙura.
Sa’ad da taimako ya katse ma,
Loton da abokai suka yashe ka,
Babu dalili na yin fargaba.
Ka dogara ga Allahnka kaɗai,
Zai ƙarfafa zuciyarka sosai.

3
Ka haƙura, ya raina, haƙura.
Masifa, mutuwa, ba ƙarshenmu ba.
Ka tuna, ƴanuwanka duka fa,
A hannun Yesu mai nasara ne.
Da mu da su ma fita duhun nan,
Ma shiga hasken Allahnmu a can.

4
Ka haƙura, ya raina, haƙura.
Haƙuri maganin duniya ne.
Talauci ne ko rashin lafiya,
Ko damuwa ko kuwa hargitsi ne,
A cikin Ruhun Allah ga murna,
A cikin ƙaunar Yesu, ta’aziyya.

Exit mobile version