Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 330 Ku Ta da Zuciyarku, Kada Ta Ɓaci Kuwa Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 330 Ku Ta da Zuciyarku, Kada Ta Ɓaci Kuwa Lyrics

 

1
Ku ta da zuciyarku, kada ta ƃaci kuwa,
Ƴanuwan ba su mutu ba, su barci su ke yi.
An shirya zamansu a gidan Sama can, Allahnmu ne ya kira su su fita duniyan nan.

2
Ba sauran zunubi, jaraba ba ta can,
Wahala duk da ƃacin rai ba za su shiga ba.
Su, Yesu su ke bi da muryar nasara,
Sunansa yana goshinsu, sun duba fuskarsa.

3
Mun ajiye jikinsu can cikin kabari
Har ran da za a ta da su marasa ruƃewa.
Shi Yesu Fansarmu, shi ne mai ba da rai,
A cikin rashin ruƃa dai, shi za ya ta da su.

4
Mun gode, Allahnmu, domin bangaskiyarsu,
Don shaidarsu a wurinmu, kwatancin halinka.
Ya Ubangijinmu, ka ƙarfafa mu yau
Domin mu bi sawunsu har mu gama aikinmu.

Exit mobile version