Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 33 Ga Yesu Ubangijinmu. Mai Ceton Duniya Lyrics
1
Ga Yesu Ubangijinmu.
Mai Ceton duniya.
Mutane, kome yawansu,
Su duk, su riƙa zuwa yabon girmansa.
2
Ku manya manya, Allah ne
Ya ba ku daraja.
Babbanku, Yesu, yana nan,
Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.
3
Ku yara duk, ku neme shi
Tun yana samuwa.
Da ƙarfi da ƙuruciya
Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.
4
Ku mata, ƙaƙa za ku yi?
Ku girmama Yesu.
Mai Ceto Almasihu ne,
Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.
5
Ku masu rashin ganewa,
Ku masu lalube,
Mai korar duhu, ga shi nan.
Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.
6
Ga Yesu Ubangijinmu,
Mai Ceton duniya,
Mutane, kome yawansu,
Su duk, su riƙa zuwa yabon girmansa.