Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 329 Ya Yesu, Rijiyar Kwanciyar Rai Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 329 Ya Yesu, Rijiyar Kwanciyar Rai Lyrics

Hymn 329 Ya Yesu, Rijiyar Kwanciyar Rai Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 329 Ya Yesu, Rijiyar Kwanciyar Rai Lyrics

 

1
Ya Yesu, rijiyar kwanciyar rai,
Sunanka ta’aziyya ne.
Kome wahalar duniya,
Kome kuwa fushin magauta,
Zuciyata ba ta ƃaci ba,
Na ƃuya cikin sunanka.

2
Sunanka gwanin daɗi ne,
Faranta zuciya ya ke yi
Ko raina duk ya duhunta,
Har ya fi dare duhu ma,
Duhuna sai shi warwatse,
Sunanka tashin rana ne.

3
Kome na rasa, ga shi nan,
Maganin kome Yesu ne.
Ban damu da talauci ba,
Ban mai da tsiya kome ba.
Tun da ban rasa Yesu ba,
Raina ya kwanta lafiya.

4
Abin da ya same ni duk,
Raini ko wulakanci kuwa,
Ƙanƙanci, kunya, damuwa,
Zalunci, ɗauri, kisa ma,
Ba zan ji tsananinsu ba,
Yesu zai tsare zuciyata.

5
Gafarar dukan laifina,
Ikon rinjayar halina,
Sakankancewar ƙaunarka,
Salama ba ta duniya ba,
An kintsa dukan cetona,
Ya Yesu, cikin sunanka.

Post navigation

Previous: Hymn 281 Yaƙi ‘Na Nan, Yaƙi Na Almasihu Ne Lyrics
Next: Hymn 554 Ya Ƴanta Mu Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version