Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 328 Tafiyarmu A Duniya Ta Kusa Ƙarewa Lyrics
1
Tafiyarmu a duniya ta kusa ƙarewa.
I, kome nisan hanya, lalle ta kai gida.
Ko duhu muka ratsa, gari zai waye can.
Babu sauran dare kuma gun Immanuel.
2
Da jinƙai duk da ilmi, ya shirya hanyata,
Har ko a cikin duhu na iske haskensa.
Zan yi yabon Mai Sani, zan yi yabon Mai Yi.
Farko ne shi da ƙarshen, shi Immanuel.
3
A zuciyar Almasihu, ƙauna ta yalwata,
Ta fi ta duniva daɗi, kome ne daɗinta.
Can Sama dai zan gane alamun ƙaunarsa.
Bisa goshina sunansa, Yesu Immanuel.
4
Amarya, idanunta a wajen ango ne,
Ai, ba ta duban wani, sai fuskarsa kaɗai.
Ni haka, fuskar Yesu da jiki sokakke,
Ɗan Rago ne zan duba, shi Immanuel.