Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 327 Mun Kawo Ƴaƴanmu, Yesu Lyrics
1
Mun kawo ƴaƴanmu, Yesu,
Kai wanda ka ke ƙaunarsu.
Ka ɗibiya musu hannunka,
Ka sa musu albarkarka.
2
Ka tsare ƴaƴanmu, Yesu,
Ka rungume su, dukansu,
Kewaye su da ƙaunarka,
Ka riƙe su da ikonka.
3
Kiyaye ƴaƴanmu, Yesu,
Ka yafe musu laifinsu,
Ka koya musu halinka,
Ka cika su da Ruhunka.
