Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 324 Sahihiyar Ƙauna Dai Ta Fi Kwatanci Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 324 Sahihiyar Ƙauna Dai Ta Fi Kwatanci Lyrics

 

1
Sahihiyar ƙauna dai ta fi kwatanci,
Mun durƙusa a gaban kursiyin,
Don waɗanda ka haɗa su su sami
Ƙauna mafificiya a zuciyarsu.

2
Rai mai jamali, kau da shakka duka,
Tabbatar da ƙauna da bangaskiya,
Da jurewa da bege da natsuwa,
Irin da ba ya saurin fushi kuwa.

3
Ba su wadatacciyar murna taka,
Da kuma kwanciyar rai da kamewa,
Iyakar kwanakinsu nan a duniya,
Har ran da za su shiga Sama can.

Exit mobile version