Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 323 A Mulkinka, Ubangiji Lyrics
1
A mulkinka, Ubangiji,
Za a tara dangogi,
Harsuna dabam dabam kuwa,
Suna yabon Almasihu.
2
Kewaye da Ubangiji,
Cerabim da Sarafim
Duk sun cika haikalinsa,
Suna rera yabonsa.
3
Darajarka, Ubangiji,
Ta ƙawata duniyan nan.
Girma, yabo, mulki, iko,
Naka duk, Ubangiji.
4
Mala’iku cikin Sama,
Tare da Ekklesiyarka,
Suna rera waƙar yabo
Zuwa Ɗan Maɗaukaki.
5
Ɗaukaka ga Allah Uba,
Mulki kuwa ga Allah Ɗa,
Iko zuwa Allah Ruhu,
Yabo zuwa Triniti.