Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 322 Ya Tsarkaka Na Allahnmu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 322 Ya Tsarkaka Na Allahnmu Lyrics

 

1
Ya tsarkaka na Allahnmu,
Yanzu kun gama yaƙinku.
Kun kwance dukan ɗaurarru,
Kun ba da su ga Allahnku.
Ya tsarkaka na Allahnmu,
Gun Yesu za ku huta yau.

2
Ya tsarkaka na Allahnmu,
Kun kai ga burinku yanzu.
Ba yunwa, babu ƙishiruwa,
Ba wuyar hanya, ba gajiya.
Ya tsarkaka na Allahnmu,
Yesu ya shirya gidanku.

3
Ya tsarkaka na Allahnmu,
Barci ya kwashe jikinku,
A ƙarewa Ɗan Allah kuwa
Zai raya ku da nasara.
Ya tsarkaka na Allahnmu,
Ga hasken Yesu wurinku.

4
Ya Allahnmu na tsarkaka,
Muna roƙo a wurinka.
Albarka ga Ubangiji
Da Ruhunsa Mai Tsarki.
Ka sada mu da tsarkaka,
Ka kai mu wurin zamanka.

Exit mobile version