Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 321 Ran da Aikinmu Ya Ƙare Cikin Wannan Duniya Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 321 Ran da Aikinmu Ya Ƙare Cikin Wannan Duniya Lyrics

 

1
Ran da aikinmu ya ƙare cikin wannan duniya,
Za mu hau mu zauna gun Mai Cetonmu,
Za mu huta daga ƙuncinmu, mu yi ta zamanmu
Wurin Yesu Kristi, Ubangijinmu.

KORUS
Za ya kira mu a Sama,
Za mu shiga gaban Allah,
Za mu wurin Mai Cetonmu,
Zuwa gidan da ya shirya dominmu.

2
Can a gida mai darajan nan, a gaban Allahnmu,
Za mu yi sujada gaban kursiyinsa,
Za mu haƙa kai da Masu Bi na dukan zamanai,
Za mu yi ta yabon Yesu, Mai Ceto.
Korus

3
Can mā gane duk dalilin ƙuncinmu a duniya,
Za mu gane yawan ceton da ya yi.
Za mu yi ta yin godiya domin dukan aikinsa,
Za mu yabi sunan Yesu, Mai Ceto.
Korus

Exit mobile version