Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 320 Sabuwar Urushalima Amaryar Yesu Ce Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 320 Sabuwar Urushalima Amaryar Yesu Ce Lyrics

 

1
Sabuwar Urushalima amaryar Yesu ce,
Mai sheƙi kamar rana, ko haske kuwa gani.
Ƙofofi na daraja, hanyar zinariya,
A cikinta ga kogi da itace na rai.

2
In kai ga wannan birni wurin da hawaye,
La’ana, bakinciki, duka sun shusshude.
Ko mutuwa da kanta an ci nasararta.
Da Ɗan Rago da Uba ɗaukakar birni ne.

3
In yi sujada tare da sauran tsarkaka.
Sa rera, Halleluya, in haɗa muryata. Kullum in yi mamaki yadda zunubaina
Ta wurin jinin Yesu, Allah ya gafarta.

Exit mobile version