Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 32 Ya Al’ummai, Ku Ɗaukaka Allah A Naku Zukata Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 32 Ya Al’ummai, Ku Ɗaukaka Allah A Naku Zukata Lyrics

 

1
Ya Al’ummai, ku ɗaukaka
Allah a naku zukata.
Ku bauta wa Madauwami,
Ku yabe shi da rerawa.

2
Ubangiji shi Allah ne,
Mahalicci sahihi kuwa.
Ya mai da mu mutanensa,
Tumakin makiyayarsa.

3
Ku shiga cikin ƙofarsa,
Da yabo shiga gidansa,
Ku gode domin jinƙansa,
Albarkaci sunansa kuwa.

4
Ubangiji kyakkyawa ne,
Jinƙansa babu iyaka,
Amincinsa ya tabbata
Tun zamanai, har abada.

Exit mobile version