Skip to content

info@example.com

Treasure Hymns – Hausa

  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page
  • Home
  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Sample Page

Hymn 317 Ga Taro Can Mai Girma Kuwa, Har Ba Mai Ƙirgawa Lyrics

  1. Home   »  
  2. Hymn 317 Ga Taro Can Mai Girma Kuwa, Har Ba Mai Ƙirgawa Lyrics

Hymn 317 Ga Taro Can Mai Girma Kuwa, Har Ba Mai Ƙirgawa Lyrics

January 10, 2026 treasurehymnsLittafin Wakoki Hausa Hymns

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 317 Ga Taro Can Mai Girma Kuwa, Har Ba Mai Ƙirgawa Lyrics

 

1
Ga taro can mai girma kuwa, har ba mai ƙirgawa,
Al’ummai, dangi, harshe duk, kowane iri kuwa,
Suna tsaye gun Allahnsu, yafe da adalci,
Ga shaida kuwa ta nasara a cikin hannunsu.

2
Sun ta da murya kuwa sun ce, ceto ga Allahnmu,
Yabo ya hau ga Allahnmu, duk da Mai Cetonmu.
Mala’iku da dattawa sun haɗa bakinsu,
Sun fāɗi bisa fuskarsu loton sujadarsu.

3
Albarka, girma, godiya, ga Allah, suka ce,
Wadata, iko, ceto kuwa, har dukan zamanai.
Yafaffun nan, ka shaida su? Daga ina su ke?
Rigunan nan da suka sa, don me walƙiyarsu?

4
Domin maganar shaidarsu, tun suna duniya,
An kashe su don suka ƙi su yi musun Yesu.
I, domin shaida ga su nan, ba shakka, ba tsoro.
Hidimar Allah za su yi dare. da rana kuwa.

5
Yunwa ba za su ƙara ji ko ƙishi ba daɗai.
Rana ba za ta buga su a gidan Allah ba.
Ɗan Allah ne mai kiwonsu, shi fa zai bi da su.
Hawaye daga idanu, Allah zai share su.

Post navigation

Previous: Hymn 4 Halittar Allah, Furta Yau Yabonku Baki Ɗaya Lyrics
Next: Hymn 412 Ga Mu Nan Shehuna Gabas Lyrics

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Hymn 346 A Cikin Farko Allah Ya Halitta Sama da Ƙasa Lyrics
  • Hymn 215 A Cikin Duniyan Nan Yanzu Lyrics
  • Hymn 218 A Cikin Dukan Halin da Mu Ke, da Murna Da Wahala Lyrics
  • Hymn 64 A Cikin Daren Nan da Aka Ba da Shi Lyrics
  • Hymn 347 A Cikin Farko Allahnmu Lyrics

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • January 2026

Categories

  • Littafin Wakoki Hausa Hymns
  • Uncategorized
Proudly powered by WordPress | Theme: goldy-mex by inverstheme.
Go to mobile version