Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 315 Zo, Mu Yabi Ƙaunar Yesu Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 315 Zo, Mu Yabi Ƙaunar Yesu Lyrics

 

1
Zo, mu yabi ƙaunar Yesu,
Jinƙansa da alherinsa.
Yana shirya mana wuri
Cikin Sama gun Uban.

KORUS
Can a Sama, wurin Yesu,
Masu bi za su taru wurinsa
Za mu rera waƙa,
Mu yabi girman sunansa

2
Lokacin da mu ke nan a duniya,
Ƴar wahala mu ke sha,
Amma ran da za mu Sama
Farin ciki za mu yi.
Korus

3
Bi shi nan da dukan zuciya,
Yi aniya cikin aikinsa.
Za mu manta da wahala
In mun shiga mulkinsa.

4
Gaba dai, mu Masu Binsa,
Har mu ga Mai Cetonmu.
Wata rana ƙofar Sama
Za ta buɗe dominmu.
Korus

Exit mobile version