Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 311 Duniyan Nan Ba Gaskiya, Duniya Tana Wucewa Lyrics
1
Duniyan nan ba gaskiya, duniya tana wucewa,
Mu, Sama mu ke so.
KORUS
Can za mu yi murna, murna, murna, murna.
Can Sama da murna, murna, murna, har abada.
2
Nan wahala mu ke sha, nan kuwa babu daɗewa,
A can ba haka ba.
Korus
3
Halin duniyan nan mu ƙi. Mu, bin Yesu mu ke yi
A duniyan nan yanzu.
Korus
4
Yabon Yesu mu ke yi, Ubangijinmu ne shi,
Can za mu gan shi kuwa.
Korus
5
Can fa daɗi za mu ji, yabon Yesu za mu yi,
Yesu Mai Cetonmu.
Korus
