Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 310 Mu Ƙanƙananan yara ne Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 310 Mu Ƙanƙananan yara ne Lyrics

 

1
Mu ƙanƙananan yara ne,
Ba ƙarfi fa, ba gwaninta.
Me za mu yi domin Yesu,
Maɗaukaki, mai girma?

2
Mun sani masu tsarki
Sun ba da ransu dominsa.
Masu aminci, tsarkaka,
Sun jure tsananin wuta.

3
Kaddararmu da tasu ɗaya,
Mu kuwa muna yin wa’adi,
Za mu bi su har mutuwa
Don Yesu, haka za mu yi.

4
Kowace rana Masu Bi
Wajibinmu ne za mu yi,
Mu kashe mugun tunani,
Mu hana aikin zunubi.

5
Loton da mu ke yin fushi,
Ko mutane sun zage mu,
Ko waɗansu sun dame mu,
Ko alfarma ta cika mu,

6
A loton nan mu tuna fa,
Mu amsa su da haƙuri,
Maganarmu da ladabi
Don yaƙin Ubangiji ne.

7
Murmushi na salama kuwa
Ya haskaka fuskokinmu.
Mu yi kome domin Yesu,
Mu ƙaunaci jama’armu.

8
Kome ƙanƙantar yara fa,
Sun iya ɗaukar giciyensu.
Aikinsu daidai ƙarfinsu,
Su yi kome domin Yesu

Exit mobile version