Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 31 Zo, Jama’a, Yabi Allah Lyrics
1
Zo, jama’a, yabi Allah,
Zo, mu kawo waƙarmu,
Yana wartsakad da ranmu,
Yana kawo cetonmu,
KORUS
Halleluya! Halleluya!
Halleluya! Amin.
2
Domin jinƙai da alheri,
Gafara da ƙauna ma,
Domin tausayi da haƙuri,
Sai mu yi ta yabonsa.
Korus
3
Kamar uba wurin ƴaƴa,
Yana jin juyayinmu,
Yana bi da kafafunmu,
Yana cin maƙiyanmu.
Korus
4
Mala’iku, ku taimake mu
Cikin yin sujadarmu.
Muna ganin fuska tasa,
Sai mu yi biyayya, mu.
Korus
5
Ranmu kamar furen jeji,
Dukanmu ciyawa ne,
Allah shi madauwami ne,
Shi kuwa ba zai sake ba.
Korus