Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 309 In Ka Karanta Cikin Matta Fa Lyrics
1
In ka karanta cikin Matta fa,
Za ka ga. jawabi, sai mu haskaka
Muddar muna nan a cikin duniya
Cetattu na Yesu, mu haskaka.
2
Amma babu dama mu haskaka
In da wani laifi cikin zuciya.
Gudu wurin Yesu, roƙi gafara.
Cetattu na Yesu, mu haskaka.
3
Mutanen da ke kewaye da mu
Suna duban hali da auyukanmu,
Kada dai su gani rashin gaskiya.
Cetattu na Yesu, mu haskaka.
4
Cikin makaranta mu shaida shi,
Ko a gida kuwa mu hana zunubi.
Cikin jinin Yesu akwai nasara.
Cetattu na Yesu, mu haskaka,
5
Cikin ikon Yesu mu bi daidai,
Dukan aikin duhu sai mu ƙi sosai,
Mutane dayawa za su gaskata.
Cetattu na Yesu, mu haskaka.