Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 308 Sunan Wani Yaro Fa, Daniel Ke Nan Lyrics
1
Sunan wani yaro fa, Daniel ke nan,
An haife shi cikin Yahudiya wata ran.
Cikin zamaninsa, Allah ne ya sa
Mutanensa su horu a ƙasar magauta.
KORUS
Tsoron Ubangiji farkon ilmi ne,
Sai mu tsaya kamar yadda Daniel ya yi.
2
Cikin aikin sarki dai, ya yi aminci.
Aka gabatad da shi ya zama sananne.
Cikin wannan duka, shaida ya ke yi,
Ba ya neman girman kansa, sai na Allahnsa.
Korus
3
Zancen yin addu’arsa, ba ya fasawa,
Kunya ba ya taƃa ji a cikin wannan ba.
Can fa wata ra na a ke ƙararsa,
Duk da haka ya yi ta addu’a kamar da.
Korus
4
Cikin ramin zakuna aka jefa shi,
Ba su iya buɗe baki ba, balle su ci.
Daniel ya kwana lafiya ƙalau,
Can da safe ya ji muryar sarki, cewa “Zo”
Korus
5
Ikon Ubangijinmu ba ya kasawa.
Har yanzu akwai shi isasshe ne dominka
Kada ka yi shakka, ko ka ji tsoro
Wurin Ubangiji dukan kome ya yiwu.