Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 307 Yara Ƙanƙanana, Ƙeta Sai Ku Ƙi Lyrics
1
Yara ƙanƙanana, ƙeta sai ku ƙi,
Daina ƙarya duka, Yesu sai ku bi.
2
Iblis mai zunubi, yara ya ke so.
Shi zai ƃata hali, yi tsayayya yau.
3
Tsare idanunku duk da kunnuwa,
Tsabtad da hannuwa, kama harshenku.
4
Yesu mai alheri yana ƙaunarku,
Yana jin tausayi, yana tsaronku.
5
Yesu ne mai ƙarfi, iko nasa ne,
Shi zai taimake ku, ku ƴaƴansa ne.