Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 304 Yesus Ya Zo Daga Sama Domin Ya Cece Ni Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 304 Yesus Ya Zo Daga Sama Domin Ya Cece Ni Lyrics

 

1
Yesus ya zo daga Sama domin ya cece ni.
Yesu ya mutu domina, Mai Cetona ne shi.

KORUS
Mai Ceto, Mai Ceto, babu Mai Ceto sai Yesu.
Mai Ceto, Mai Ceto, babu Mai Ceto sai shi.

2
Ni ma nan gaba zan bi shi, zunubi sai in ƙi.
Yesu kuwa zai taimake ni, abokina ne shi.
Korus

3
Kome jaraba ta tashi, ba za ta ei ni ba,
Don idan na roƙi Yesu, shi za ya fizge ni.

Korus
4
Kome yanzu ya dame ni, Mai Cetona ‘na nan,
Shi kuma zai kiyaye ni a cikin duniyan nan.
Korus

Exit mobile version