Littafin Wakoki Hausa Hymns
Hymn 303 Yesu Yana Ƙaunarmu, Wannan Na Sakankance Lyrics
1
Yesu yana ƙaunarmu, wannan na sakankance.
Gaskiyarsa ta tabbata, Allah ne ya shaida shi.
KORUS
I, yana sonmu, i, yana sonmu,
I, yana sonmu, Yesu Mai Cetonmu.
2
Yesu yana ƙaunarmu, mutuwarsa ta keƃe mu.
Shi ya shafe zunubai, shi ya buɗe ƙofar rai.
Korus
3
Yesu yana ƙaunarmu, za mu tafi wurinsa,
Za mu gan shi jim kaɗan, can a Sama gun Uban.
Korus
4
Yesu yana ƙaunarmu, ko mā ƙi mu bi shi nan?
Kome yawan wahala, ba ma fasa ƙaunarsa.
I, muna sonsa, i, muna sonsa,
I, muna sonsa, Yesu Mai Cetonmu.