Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 302 Ƙauna daga Allah Ce, Wannan Na Sakankance Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 302 Ƙauna daga Allah Ce, Wannan Na Sakankance Lyrics

 

1
Ƙauna daga Allah ce, wannan na sakankance,
Batun nan na Yesu ne, Allah ƙauna ne.

2
Ƙauna ba ta jin kishi, ba ta rashin hankali,
Tana kuwa da haƙuri, Allah ƙauna ne.

3
Tana kuwa da nasiha, ƙauna ba ta kumbura,
Ba ta kuwa jin cakuna, Allah ƙauna ne.

4
Ƙauna tana jurewa, ƙauna ba ta nukura,
Haka cikin abu duka, Allah ƙauna ne.

5
Allahna, ƙaunatacce, kyautar ƙauna taka ce,
Ba ta ƙarewa daɗai, Allah ƙauna ne.

Exit mobile version