Site icon Treasure Hymns – Hausa

Hymn 301 Alherin Ubangijina Abin Mamaki Ne Lyrics

Littafin Wakoki Hausa Hymns

Hymn 301 Alherin Ubangijina Abin Mamaki Ne Lyrics

 

1
Alherin Ubangijina abin mamaki ne.
Yesu ya ba da jininsa pansar mai zunubi,
Pansar mai zunubi.

2
Tun ranar da na tuba fa, alherinsa ‘na nan.
Alheri kuwa zai kai ni can wurin Ubangiji,
Wurin Ubangiji.

3
Ya raina, kar ka manta dai da duk alherinsa.
Abu duk da ke cikina ya yabi sunansa, Ya yabi sunansa.

4
Ubangiji da tausayi da jinkirin fushi ne.
Alherinsa tun farko ne a kan mai tsoronsa,
A kan mai tsoronsa.

5
Me zan bayar, Ubangiji, domin alherinka?
Zan miƙa jiki hadaya tare da zuciyata,
Tare da zuciyata.

6
Ruhun Alheri, zuga ni, tsabtad da gurina.
Iyad da ni don aiki na shelar bishararka,
Shelar bishararka.

Exit mobile version